Sakamakon
wani bincike da aka gudanar a jihar Lagos ya nuna cewa yanzu haka da
yawa daga cikin Maza suna tsoron cewa Matan su za su iya kashesu.Wannan
sakamakon ya fito ne bayan matsalar da aka samu tsakanin marigayi
Bilyamin da matarsa Maryan lamari da ya zama babban labari a kafofin
watsa labarai a Najeriya.
Wani kididdiga da Gwamnatin
jihar Lagos ta fitar dangane da adadin yawan koke da ake samu sakamakon
tashin hankali tsakanin Ma'aurata a jihar ya nuna cewa Mata ne suka fi
shan wuya a wannan lamari domin a cikin koke 852 da aka gabatar a
tsakanin watanni tara da suka gabata 55 ne kawai Maza suka shigar yayin
da sauran Mata ne suka koka.
Wata ma'aikaciyar Asibiti a
garin Birnin Kebbi da bata son a ambaceta ta shaida wa ISYAKU.COM cewa
"Ni a nawa fahimta ,Mata ne ke jawo lamarin da ke kaiwa ga tashin
hankali ko fitina a cikin gida,domin idan har kina bin Maigidan ki sau
da kafa, babu yadda za'ayi har ace yau lamari ya kazamce har ya kai ga
tashin hankali".
"Da farko dai Mace bata da hurumin
binciken wayar Mijinta idan har Matar gaskiya ce mai son zaman lafiya,
na biyu raini da neman ganin laifin Miji, sai wulakanta miji ta hanyar
cin mutunci ko rashin ragowa wajen furta kalamai.Sakamakon haka Miji zai
iya tunzurewa musamman ga Mata wadanda ke kaiwa ga cukume rigar
Maigida, ka ga daga nan raini ya shiga shi kuma Maigida dole ne ya
kubuta sakamakon haka sai dambe da tashin hankali ya kaure" .
Duk
da yake wannan lamari ya zama ruwan dare a ko'ina cikin fadin Najeriya,
amma kasancewar irin wannan lamarin ya fi yawa a Arewacin Najeriya,
idan baku manta ba,mun kawo maku labarin wata mata da ta tafasa ruwan
zafi ta zuba wa Mijinta da Amaryarsa a jihar Kaduna yayin da suke barci
wai domin ya yi mata kishiya lamari da ya sa Mijin ya rasa ransa kwanaki
kadan bayan jinya.
Haka zalika mun kawo maku labarin
Matar da ta caka wa Mijin ta wuka sakamakon yunkuri da ya yi na kara
aure wanda hakan ya zama ajalinsa a jihar Niger.
A
jihar Kano kuwa mun kawo maku labarin wacce ta kashe maigidanta bayan ta
saka masa abincin bera a cikin nashi abinci sakamakon haka ya mutu.
Haka
zalika ga labarin Bilyamin da Maryam da ta kashe Bilyamin a gidansu da
ke Wuse a Abuja da kuma labarin wadda ta kwada wa mijinta kwalba a kai
sannan ta yi amfani da tsinin kwalbar ta caka masa a kirji a jihar
Zamfara.
Ina mafita ne akan wannan lamari ? rashin
aiwatar da hukunci ne ko kuwa son ra'ayi ne ke samar da tunani balle
dama da ke sa mutum ko mace ta yi tunanin cewa za ta iya kashe
maigidanta kuma babu abun da zai faru ?.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari