Dan shekara 51 ya yi wa yar shekar 6 da 5 fyade a Argungu,yan kare hakkin bil'adama sun shigo

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Duniya, wanda wakilinta na jihar Kebbi Barista A.A Fingilla, tare da hadin guiwa da kungiyar kare hakki, tare da jin dadin yara kanana a jihar Kebbi, watau International Human Rights Commission tare da Equity Destitute Child Right and Welfare Initiative, wanda shugabanta Fatima Muhammed Kabir tare da manbobin kungiyar sun dira garin Argungu na jihar Kebbi, domin tattaunawa da iyalan wasu yara kanana guda biyu yan shekara 6 da 5 da ake zargin wani mutum mai suna Yusuf Dan galadima ya yi masu fyade.

Wanda aka kama da tuhumar aikata wa kananan yaran fyade magidanci ne mai shekara 51, mai auren mata biyu da yara goma sha takwas (18) dan garin Tungar Gwari.

Kungiyoyin sun tabbatar wa iyayen yaran wadanda yara mata ne kanana, cewa yanzu kungioyoyin sun shigo cikin tsarin ganin an yi wa kananan yara mata da ake zargin Yusuf ya yi wa fyade adalci a fuskar Kotu.

Majiyar mu ta labarta mana cewa bayan Yusuf ya aikata fyade ga yarinyar, zancen ya kai ga jami'an tsaro na NSCDC a garin Argungu, wadanda suka gudanar da aikin bincike, bayan sun kama Yusuf. Jami'an sun kai yaran babban Asibitin gwamnati, inda sakamakon gwajin kimiyya da aka gudanar ya nuna cewa an keta budurcin yarinyar mai shekara 6 tare da samun maniyi.

Sakamakon haka hukumar ta gurfanar da shi a gaban Kotu, kuma daga bisani Kotu ta tasa keyarsa zuwa Kurkuku kafin ranar da za ta sake zama kan shari'ar da ake yi masa.

Wata majiya har ila yau, ta labarta mana cewa wanda ake zargi da aikata fyaden, ya dade yana aikata irin wannan danyen aiki a cikin al'umma, amma saboda rashin kwakkwarar shaida lamarin ya dinga jan kafa kafin dubunsa ta cika. Majiyarmu ta yi zargin cewa bai bar yan mata ba, yanzu kuma har da yan yara kanana. Hakazalika majiyar ta ce har ikirari da fariya wanda ake zargin yake yi kan aikata wannan danyen aiki.

Babban Lauya mai wakiltar hukumar kare hakkin bil'adama a jihar Kebbi, Barista A. A Fingilla, ya sha alwashin cewa " Za mu jajirce domin ganin cewa wanda ya aikata irin wannan danyen aiki ya fuskanci hukuncin abin da ya aikata. Yanzu mun shigo sosai cikin wannan lamari kuma za mu ci gaba da ganin mun yi abin da ya kamata tare da hadin guiwa da kungiyar kare hakkin tare da jin dadin yara".

Barista A.A Fingilla tare da Fatima Muhammed Kabir shugaban kungiyar kare hakki tare da jin dadin yara da sauran manbibin kungiyar ne suka kai ziyara a gida yara kanana da aka keta hakki tare da mutuncin su a garin Argungu ta hanyar zargin aikata fyade a kansu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN