Abin kunya: An kama matashi da ya yi lalata da wata karya ta mutu

An gurfanar da wani matashi mai suna Boniface Mutuku Munyao a gaban wata Kotu, bisa zargin yin lalata da wata Karya a yankin Kangundo da ke gunduman Machalos a kasar Kenya ranar 8 ga watan Janairu 2020.

ISYAKU.COM ya samo cewa Mutuku ya dade yana aikata wannan danyen aiki da karyar, amma bayan ya aikataa wannan lalata da karyar ranar 8 ga watan Janairu, sai ya kasheta ta hanyar shaketa bayan ya daureta da igiya.

Rahotanni sun ce an sami kwararon roba (condom) da dama a wani tsohon gida wanda mallakan Kakar Mutuku ce kuma waje da yake aikata lalata da karyar kafin ya kasheta.

Basaraken garin mai suna Bethwel King’ele, ya ce, " An kama Mutuku dumu dumu yana lalata da karyar, bayan makwabta sun ji wani wari mai tsanani yana busowa daga cikin gidan. Sai jama'a suka shiga domin su gan abin da ke faruwa".

Basaraken ya kara da cewa " Watakila Mutuku yana cikin mayen miyagun kwayoyi ne lokacin da yake aikata wannan danyen aiki".

Sai dai Alkalin Kotun Majistare D Orimba, ya bayar da belin Mutuku a kan kudin kasar Kenya Ksh100, 000 kudi kasa. Ya daga shari'ar zuwa ranar 22 ga watan Janairu 2020.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN