Jami'an tsaro sun halaka wata fitacciyar gwanin kisa na kungiyar masu hada hadar miyagun kwayoyi a kasar Mexico da ake kira Jalisco New Generation Cartel. Yar shekara 21 Maria Guadalupe Lopez Esquivel wacce ake wa inkiya da "La Catrina" ta shahara wajen amfani da miyagun bindigogi tana daukan hotuna wadanda take sakawa a shafukanta na sada zumunta.
Ta gamu da ajalinta ne a wani samame da jami'an tsaron kasar Mexico da suka hada da soji, Dakarun tsaron kasa (National Guard) da yansandan jihar Michoacin suka kai a wani gida da ake tafiyar da harkar kungiyar a asirce.
La Catrina wacce ta kasance a tsorace kuma ta rude bayan albarussai sun sameta, sakamakon haka fuskanta da tufarta ya jike da jini lokacin da take kokarin neman iskar shakawa kafin isowar jirgi mai saukar angulu da ya zo domin kaita asibiti amma ta mutu mintoci kadan a cikin jirgin.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari