Rahotun Legit Hausa
Mahaifiyar saurayi Suleiman ta amince dan ta ya bi wata baturiya mai shekaru 45 wacce tsuntsun soyayya ya daukota daga Amurka domin haduwa da masoyinta da suka hadu a kafa sada zumuntar zamani ta Instagram.
Baturiyar birnin California din tazo daga Amurka har unguwar Panshekara dake Kano, domin tabbatar da soyayyar ta ga matashi Suleman mai shekaru 32.
Sun hadu ne a kafar sada zumunta zamani ta Instagram ne da matar. A halin yanzu, daga an kammala shirye-shirye zata saka masoyin nata a gaba su wuce kasar Amurka.
Fatima Suleiman wacce ita ce mahaifiyar saurayi Suleiman, tace bata da suka a kan lamarin. Ta amince danta ya bi masoyiyar tasa zuwa kasar Amurka.
Ango Suleiman kuwa yace shi dama bashi da burin da ya wuce ya haifa yara ruwa biyu masu masifar kyau kalar turawa. Ya kuma yi alkawarin zai dinga kawo ziyara Najeriya don gaisawa da ‘yan uwa da abokan arziki.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari