‘Yan Sanda za su daina gurfanar da masu laifi a kotu – Gwamnatin Kano

Rahotun Legit Hausa

Gwamnatin jihar ta bada wannan sanarwa a Ranar Lahadi, 29 ga Watan Disamba, 2019, ta bakin Kwamishinan shari’a, Ibrahim Mukhtar. Ibrahim Mukhtar wanda shi ne babban Lauyan gwamnatin jihar Kano ya bayyana cewa an yi wa dokokin jihar Kano wasu kwaskwarima.

Mukhtar ya ce an kawo wadannan cigaba a harkar dokokin laifuffuka ne domin karfafa bangaren shari’a, kamar yadda mu ka samu labari. A cewarsa, gwamnatin ta dogara ne da sashe na 221 na kundin tsarin mulki wajen haramtawa ‘Yan sanda shigar da kara a madadin jihar.

Haka zalika Kwamishinan ya ce sun yi la’akari da sabuwar dokar laifuffuka a kokarin su na yi wa ayyukan ‘Yan Sandan kasar garambawul. “Mu na kokarin karbe gaba daya sha’anin gurfanar da Mai laifi a gaban kotu daga hannun ‘Yan Sanda a jihar.” Inji Hon. Ibrahim Mukhtar Kwamishinan ya ce: “Tun da aikin ‘Yan Sanda ya kunshi gano laifi da bincike da hana laifuffuka, za mu taimaka masu wajen wannan aiki."

“Sai ka ga cewa Masu laifi su na damar daukar hayar har manyan Lauyoyi na SAN yayin da hukuma ta dogara da Lauyoyin ‘Yan Sanda.” Kwamishinan ya ke cewa Lauyoyi da ke tsayawa gwamnati su na da karancin ilmi don haka su ke neman ganin an gyara wannan lamari.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN