Yar shekara 13 ta mutu wajen nakudan cikin shege da mahaifinta ya yi mata

Wata yarinya yar shekara 13 mai suna Launa Ketlen, ta mutu yayin da take nakudan haihuwar cikin da mahaifinta mai suna Tome Faba mai shekara 36 ya yi mata, kamar yadda yansanda suka sanar a kasar Brazil'

Launa Ketlen wacce yar makaranta ce, ta sha muzgunawa har tsawon shekara 4 a wajen mahaifinta inda yake saduwa da ita tun tana yar shekara 9 kamar yadda binciken yansanda ya samo.

An garzaya Asaibiti da Ketlen bayan ta koka kan matsanancin ciwon ciki da ke damuwarta, sakamakon haka Likitoci suka gano cewa tana dauke da juna biyu, kuma suka dauki matakin ganin ta haihu, daga bisani ta haifi Jariri.

Bayan mako daya, Likitocin sun garzaya zuwa wani babban Asibiti da Ketlen a cikin jirgin sama bayan yanayin lafiyarta yana kara tabarbarewa, amma sai ta mutu a kan hanyar zuwa birnin Manaus mai nisan kilomita 363.

Shugaban yansandan birnin Coari watau Jose Barraadas ya ce, yansanda sun kama Tome Faba bayan ya tsere, kafin daga bisani suka cafke shi kuma suna bincike a kan lamarin.


DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN