Karban albashi sau 2 a wata: Gwamnatin Zamfara za ta gurfanar da ma'aikata 108 a Kotu

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce za ta gurfanar da ma'aikatan gwamnatin jihar guda 108 wadanda aka gano suna karbar albashi a wurare biyu a ma'aikatun jihar. Kwamishinan kudi na jihar Alhaji Rabi'u Garba ne ya shaida wa manema labarai haka a Gusau ranar Lahadi.

An gano wadanda suke karbar albashi sau biyu ne a ma'aikatu daban daban a fadin jihar.

Garba ya ce hakan ya biyo bayan wani bincike ne da ake gudanarwa kan matsalolin albashin ma'aikatan jihar Zamfara karkashin shugabancin Gwamna Bello Matawalle. Ya kuma ce ba wai ana yin haka bane domin a ci zarafin kowa, ko bita da kulli, amma an yi haka ne domin a kawo sa'ida a aikin gwamnatin jihar.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN