Yadda aka kama wata matar aure turmi tabarya da wani kwarto suna lalata

Rahotanni daga Southlea Park a birnin Harare, sun ce an kama wata matar aure tare da wani matashi suna lalata a cikin daren Juma'a bayan maigidanta ya dawo ba zato ba tsammani.

An kama matar mai suna  Loveness Nyahwema tsirara tarae da saurayinta mai suna Stephen Mapfurutsa, shi ma tsirara turmi tabarya suna zina.

Mijin Nyahwema mai suna Alois Mugomba, ya dawo ne cikin dare bayan an tsegunta masa cewa wani kato yana tare da matarsa a cikin gidansa. Lamari da aka ce sun dauki lokaci suna harkarsu idan mijinta ya tafi wajen aiki da dare.

Alois Mugomba yana da mata biyu, amma makwabta sun sha gaya masa cewa matarsa Nyehwema tana harka da wani kato, amma Alois bai yarda ba sai yanzu da Allah ya bayyana masa da idonsa ya kamasu tare da sauran makwabta turmi tabarya.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post