Yanzu-Yanzu: Majalisar jihar Kano ta amince da kudirin karin masarautu a jihar Kano

Legit Hausa
A yau Alhamis ne majalisar jihar Kano ta amince da bukatar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta kirkirar sabbin masarautu a jihar Kano. Gwamnan na bukatar karin masarautu hudu ne don mayar da jimillar masarautu biyar a jihar.
An mika bukatar ne ga majalisar jihar Kano din a ranar Litinin, wacce ta samu karatu kashi na uku a safiyar yau Alhamis. A take kuma aka maida bukatar ta zama doka.
Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa, an gyara bukatar ne a sashi na 12 kadai, wanda 'yan majalisar suka saka cewa, sai gwamna ya nemi amincewarsu kafin ba Sarakunan matsayi na daya, biyu da kuma uku.
Bayani dalla-dalla na zuwa nan gaba.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari
Previous Post Next Post