DSS ta saki Sowere ta biyashi taran N100.000

Hukumar tsaro na farin kaya DSS ta saki dan jarida mai shafin Saharareporters .com  Omoyele Sowere bayan ya shafe kwanaki 126 a tsare.

Gwamnatin tarayya ta cafke Sowere bayan ya yi kokarin jagorantar taron tattaki  mai lakabin Juyinjuyihali #RevolutionNow wanda gwamnati ta ce haramtacce ne.

Jastice Ijeoma Ojukwu ya ce hukumar DSS bata da wani dalili na ci gaba da tsare Sowere duk da yake ya sa hannu a warantin sakinsa.

Lauyan Sowere Femi Falana, ya tabbatar da haka, ya kuma kara da cewa DSS ta biya Sowere N100.000 zaman taran Kotu na ci gaba da tsare shi bayan umarnin sakinsa.

Sowere ya cika sharuddan belinsa tun ranar 6 ga watan Nuwamba, amma ba a sake shi ba. Tun ranar 3 ga watan Agusta da jami'an DSS suka kama shi a Lagos yake hannun hukumaar DSS. 

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN