Wakar siyasa: Wasu Mawakan jihar Kebbi sun sha dan banzan duka | ISYAKU.COM

Da misalin karfe 2:00 na dare ranar Lahadi, wasu da ake zargin yan daban siyasa ne , sun je garin Gwadangaji suka dauko Mawaki Bello Bala Aljannare daga gidansa suka yi awon gaba da shi zuwa gidan wani dan siyasa a cikin Birnin kebbi, inda ya fuskanci dukan fitan albarka har da barazanar kisa kamar yadda majiyarmu ta shaida mana.

Hakazalika an balle dakin Otal da sauran mawakan suka sauka a cikin garin Birnin kebbi kuma aka dauko su aka kaisu gidan wannan dan siyasa da karfe 3 na dare inda aka kai Bello Aljannare, su ma a nan ne suka sha dan banzan duka na fitan hankali.

Majiyarmu ta samo cewa an yi masu wannan duka ne sakamakon wata wakar diban albarka da Mawakan suka yi ma wani babban dan siyasa a jihar Kebbi. Lamari da ya tayar da kura ganin yadda dubun dubatan mutane suka mallaki wannan wakar cikin yan kwanaki kalilan.

Sai dai tuni wannan labari tare da hotunan mawakan da aka yi ma duka ya bazama cikin yanar gizo da shafukan sada zumunta, lamari da ya zama abin tattaunawa a fagen siyasar jihar Kebbi a yanzu.

Mujallar ISYAKU.COM ya samo yadda fuskokin wasu daga cikin mawakan ya kumbura sakamakon zargin duka, hakazalika shafin duka ya bayyana a jikin Mawakan.

Amma bincike da muka gudanar, ya nuna cewa, a halin yanzu Mawakan basu shigar da kara ba ga hukumomin tsaro kawo yanzu. Sai dai wasu masu fashin baki kan lamurran siyasa sun tabbata mana cewa, ba mamaki Mawakan ba za su yi kara ba, ganin cewa sun yi amfani da munanan kalaman batanci ga wani babban dan siyasa a jihar Kebbi.

A ranar Asabar da ta gabata, wani Mawaki ya sake sakin wata wakar Gambara, wanda a ciki ya zazzage buhun barkonon batanci ga wani babban dan siyasa, wanda masu fashin baki suke ganin lamarin ya wuce abin da hankali zai dauka.

Wani jami'in tsaro da baya son a ambaci sunansa, ya yi mana fashin baki cewa " Ina zargin cewa wannan lamari daukan fansa ne daga wasu yan daban siyasa, idan Mawakan basa son babban dan siyasan saboda sun sami matsala da shi, ai akwai wasu matasa ko yan daban siyasa da suke sonsa kuma za su iya aikata komai domin kare martabar shi".

Majiyar mu ta samo cewa Mawakan sun ce su fa yanzu aka fara, domin ba gudu ba ja da baya. Sai dai abin da ake tsoro shine yadda lamurra ke neman kazamcewa zuwa daukan doka a hannu daga bangarorin guda biyu.

Yanzu haka jama'ar jihar Kebbi, sun sa ido su gan yadda lamarin zai kaya tsakanin bangarorin guda biyu, ko Mawakan za su ci gaba da sakin wakokin batanci ko hannunka mai sanda, ko kuma magoya bayan dan siyasan za su dinga sa yan daba su yi wa Mawakan duka da karfin tsiya, marmakin fahimtar juna a daidaita domin ciyar da jihar Kebbi gaba, ko jawo ababen kunya da ke yawan zubar da martaban jihar Kebbi a idanun jihohin arewacin Najeriya, da Najeriya ita kanta har da Duniya gaba daya.

Yunkuri da muka yi domin jin ta bakin P.A na babban dan siyasan kan lamarin ya ci tura, domin bai amsa kiraye kirayen yan Jarida da yan rahotu ba, hakazalika bai amsa sakon SMS ba kafin rubuta wannan rahotu.

DAGA ISYAKU.COM

Rubuto ra'ayinka ko ka tuntube mu. Latsa nan

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post