Magida ya kone matarsa da ruwan zafi domin tana gaisawa da makwabcinsa

Wani magidanci mai tsananin kishi mai suna Mr Michael Essien ya yi wa matarsa mugun duka sakamakon haka ya yi mata munanan raunuka a birnin Ikko watau Lagos.

Essien dan shekara 42 ya dawo ne sai ya tarar da matarsa Mariam a cikin dakin dafa abinci watau Kitchen, tare da wani matkwabcinsa da ya tsaya ta tagar dakin dafa abinci yana magana da Mariam wacce ta dora ruwan zafi a wuta domin ta tuka tuwon Semovita.

Ganin haka ke da wuya sai lamarin ya zama rigima da ya sa Essien ya yi wa Mariam duka daga bisani ya dauko tafasashshen ruwan zafi da ta dora a wuta domin ta tuka tuwo ya kwara mata a jikinta, wanda hakan ya haifar mata da munanan raunuka sakamakon konewa da ruwan zafi.

Jami'ai daga rudunar yansanda na Isolo sun kama Essien kuma ya amsa laifinsa lokacin bincike na yansanda. Majiyar isyaku.com ta ce yansanda sun gurfanar da Essien a gaban Kotu.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post