Adam A. Zango ya mayar da harkokinsa Kudancin Najeriya

Legit Hausa

Sanannen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya
shaida wa Aminiya cewa zuwa yanzu ya koma birnin Legas da harkokinsa.
Jarumin ya ce, Ya koma can ne don bunkasa harkokinsa a kan yadda ya
tsaya Arewa,

"komawa ta Legas kamar wanda ya yi makarantar sakandare
ne idan yana son cigaba da karatunsa sai ya nufi jami'a, wannan shi ne
abinda nayi".

Zango ya kara da cewa, irin karan tsanar da abokan
sana'arsa suka aza masa yana cikin dalilinsa na yin kaura zuwa Legas.
Sanannen abu ne rikice-rikicen da suka taru suka yi katutu a
masana'antar fina-finan hausar.

Tuni jarumin ya wallafa fitarsa daga masana'antar a shafinsa na Instagram. Bayan nan kuwa, ya fito ya bayyanawa jama'a cewa zai cigaba da yin fina-finansa amma za a iya
kallonsu ne kai tsaye ta kafar YouTube. Hakanne kuwa ya faru, domin
jarumin ya shirya fina-finansa inda ya wallafa su a kafar YouTube don
cigaba da nishadantarwa tare da ilimantar da masoyansa.
Previous Post Next Post