"Wakar batancin siyasa a Kebbi ba da sanina ba" Mawakiya Habiba Zuru ta rera sabuwar waka | ISYAKU.COM

A ci gaba da kokari da wasu ke yi na yayyafa wa kura da wakar manyan mawakan jihar Kebbi suka yi ma wani babban dan siyasa a jihar Kebbi ya tayar, bayan raddin matasan mawakan jihar Kebbi, wata fitacciyar mawakiya Habiba Zuru, ta ce ita kam ba butulu bace domin an yi mata gomman arziki karkashin Gwamnatin jihar Kebbi mai mulki karkashin jam'iyar APC.

Habiba Zuru wacce ita ce Kodineta na kungiyar Creative Industry Group na jihar Kebbi, kuma shugaba ko Chairperson na Arewa Film Makers Association AFMAN reshen jihar Kebbi, ta ce:

"Ni yar uwarta ban san ta shiga cikin wannan harka ba, kuma ba da shawara ta ba, idan aka yi mani alhairi kamar an yi mata ne. Kuma ko ita din an yi mata. Mahaifiyarmu tana godiya, kuma tana gaida Gwamna Atiku Bagudu. Ita ta haife ni kuma ta haifi Jamila. Ba a yi shawara da ni ba, yadda kowa ya ji wannan waka haka na ji shi"

Habiba ta rera wata waka inda ta fayyace tsakaanin fari da baki, da kuma waiwaye ga ababe da ta ce sun faru a baya dangane da lamarin da ake takaddama a kai.

Ta kuma tabbatar mana cewa, an kai ta aikin Hajji tare da mahaifiyarta, an kuma bata motoci sakamakon waka da ta yi, sakamakon haka ta ce babu yadda za a yi ta butulce wa gaskiya.

SAURARI WAKAR MARTANI DA HABIBA TA RERA

Latsa nan ka sauke sauti

ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post