Boko Haram sun kashe kwamandan sojin Najeriya a filin daga

Legit Hausa

Wani babban kwamandan yaki na rundunar Sojan kasa ta Najeriya ya gamu
da ajalinsa yayin da mayakan kungiyar ta'addanci na Boko Haram suka
dasa wani bom a kusa da motarsa wanda ya tashi da shi, inji rahoton
Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a
garin Marten a jahar Borno kamar yadda wasu majiyoyi na karkashin kasa
daga rundunar Sojan suka tabbatar, inda suka ce jami'in Sojan shi ne
kwamandan bataliya ta 153 dake Marte.

Majiyoyin sun kara da cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, 7 ga watan Disamba yayin da kwamandan yake jagorantar Sojojinsa zuwa aikin sintiri, a daidai
wannan lokaci ne bom din ya tashi da motar kwamandan.

Wasu majiyoyi na daban sun tabbatar da mutuwar kwamandan, amma sun ce babu tabbacin ko
shi kadai ne ya mutu, ko kuma akwai wasu Sojoji na daban basu mutu ba,
sai dai majiyarmu ta ki bayyana sunan mamacin sakamakon babu tabbacin
ko iyalansa suna da masaniya ko kuwa a'a.

A wani labarin kuma, akalla dan Boko Haram daya ne ya gamu da ajalinsa a sakamakon wata arangama da aka yi tsakanin dakarun rundunar Sojin Najeriya tare da mayakan
kungiyar ta'addanci na Boko Haram a jahar Borno. Jami'in kula da watsa
labaru na Operation Lafiya Dole, Kanal Aminu Iliyasu ne ya sanar da
haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba
inda yace an yi dauki ba dadin ne a kauyen Malam Fatori cikin karamar
hukumar Abadam na jahar Borno.

Kanal Aminu yace dakarun runduna Soja ta 68/94 ne suka kaddamar da samame a mafakar yan ta'addan Boko Haram dake kauyen, wanda hakan yasa bayan sun sha wuta yan ta'addan suka
ranta ana kare, amma Sojoji basu kyalesu, sai da suka musu rakiyar
Kura.
Previous Post Next Post