Kotu a jihar Adamawa ta daure Likitan bogi shekara 54 a Kurkuku

Wata babban Kotu da ke zamanta a garin Yola babban birnin jihar Adamawa, ta daure wani Likitan bogi mai suna Ibrahim Mustapha tsawon shekara 54 a Kurkuku.

Jastis Natha Musa na babban Kotu ta 1, ya yanke wa Ibrahim Mustapha hukunci bayan ya yi la'akari da koken Likitan na bogi kafin ya yanke masa hukunci.

Alkalin ya ce ya yi la'akari har ila yau da roko da Lauyan Ibrahim ya yi wa Kotu kan neman sassauci a hukuncin, ya kuma yanke masa hukunci bisa laifuka 9 da aka same shi da laifi.

Alkalin ya ce " A tuhuma ta 1 zuwa 3, na yanke masa hukuncin daurin wata 6 a kowane laifi da zabin biyan taran N20.000 kowanne. A tuhuma ta 8, Kotu ta daure shi tsawon shekara 3 ko biyan taran N50.000.

Sai dai a sauran laifukan, Alkalin ya ce "A tuhuma ta 4,5,6,7 da 10, na yanke masa hukunci daurin shekara 10 kowanne ba tare da zabin tara ba". Jastis Nathan ya ce mai laifin zai yi zaman Kurkukun ne gaba daya.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post