Safeton yansanda ya bindige kofur har lahira a Abuja,ya harbi suparitanda ya kashe kanshi

Wani mumunan lamari ya faru ranar Asabar 21 ga watan Disamba bayan wani safeton yansanda ya bindige wani kofur na yansanda har lahira, kuma ya harbi wani suparitanda na yansanda kafin ya juya bindiga ya bindige kansa har lahira a ofishin yansanda da ke Dutsen Alhaji a babban birnin tarayya Abuja.

Majiyar mu ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin Asabar

Kakakin hukumar yansanda na birnin tarayya Abuja Maryam Yusuf, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma kara da cewa Kwamishinan yansanda na birnin tarayya, ya nuna alhini tare da takaicin yadda hakan ta faru. Daga bisani ya bayar da umarni a gudanar da binciken sirri kan dalilin faruwar lamarin.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post