Mutum 6 sun mutu yayin da wasu da dama suka sami raunuka sakamakon ruftawan wani rami da ake hakan ma'adinai a garin Zawan da ke karamar hukumar Jos ta kudu.
Rahotanni sun ce ana gudanar da aikin hakan ma'adinan ne ba bisa ka'ida ba, kuma wadanda suka mutu matasa ne masu shekar 20 zuwa 27.
Akalla mutum 50 ke cikin karkashin ramin kafin ruftawansa, wanda aka ce shi ne farko a garin.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari