Gwamnan jihar Kano Umar Ganduje ya ba Mai martaba Sarki Muhammad
Sanusi na 3 kwanaki 2 ya yi nazari kuma kuma ya amince da mukamin da ya
bashi na shugaban majalisar Sarakuna.
Idan baku manta
ba, an sha samun takun saka tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi a
baya. Rigingimu da har yanzu an kasa shawo kansu, duk da yake a baya
manyan mutane a ciki da wajen jihar Kano sun yi kokarin sasanta
bangarorin guda biyu.
Jaridar Legit Hausa, ta ruwaito
cewa, ranar 9 ga watan Disamba, 2019, gwamnan ya nada Sarkin Kano
matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar amma har yanzu Sarkin bai
furta uffin kan tayin ba. A wani wasika da aka aikawa fadar sarkin daga
ofishin babban sakataren gwamnatin jihar, gwamna Ganduje ya bukaci
sarkin yayi martani kan tayin da akayi masa cikin kwanaki biyu da karbar
wasikar.
Wasikar na dauke da kwanan wata 19 ga Disamba,
2019. Sai dai wasu na keke da keke da Sarki Sanusi sun ce har yanzu
Sarki bai yi ido biyu da takardar nadin ba ballantana ya mayar amincewa
ko watsi da mukamin shugaban majalisar sarakuna ba.
A
bangare guda, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar
Alhamis ya bayyana cewa ya samu wasika daga kungiyoyin fafufutuka 35
inda suka bukaci ya kwancewa sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu,
rawani kan rashin biyayya.
Mai magana da yawun Ganduje,
Abba Anwar, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki inda ya bayyana
cewa kungiyoyin sun nuna damuwarsu kan yadda sarkin ke kokarin kafa wata
jihar cikin jihar Kano. Abba Anwar bai lissafa sunayen kungiyoyin ba
amma ya ce shugabansu Ibrahim Ali, ya rattafa hannu kan wasikar.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari