Aikin Jarida da SMedia: Sakataren gwamnatin jihar Kebbi Babale ya zazzage bayani

Isyaku Garba Zuru 18-12-2019

Gwamnatin jihar Kebbi tare da hadin guiwa da kungiyar yan Jarida na kasa Nigerian Union of Journalists NUJ, da De-MAz Consultancy, ranar Laraba18 ga watan Disamba, sun gabatar da taron bita da sanin makamar aiki ga yan Jarida da masu amfani da kafofin sada zumunta Social Media SMedia domin tunatarwa tare da karin fahimta yadda za a yi amfani da kafofin sadarwar sada zumunta domin inganta sahihancin labari da za a dinga watsawa. Taron ya sami halartar yan Jarida da yan SMedia daga kananan hukumomi da garin Birnin kebbi.

Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu, wanda Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi Babale Umar ya wakilta, ya ce " Gwamnati a shirye take ta amsa tambayoyin yan Jarida, amma ba wai ta amsa tambayar ra'ayi ba. Za a iya tuntuban jami'an watsa labari ko Daraktan watsa labarai na ma'aikatan watsa labarai domin amsa tambayoyin manema labarai.

Idan manema labari basu gamsu da bayanin jami'an ko Darakta ba, za su iya zuwa wajen Sakataren din-din-dim na ma'aikatar, ko zuwa wajen Kwamishinan watsa labarai, idan har ila yau ba a sami gamsuwa ba, za a iya zuwa wajen Sakataren Gwamnati SSG, daga karshe idan haka bata ci ma ruwa ba , za a iya zuwa wajen Gwamna wanda a shirye yake a ko da yaushe ya amsa tambayoyin manema labari a jihar Kebbi".

Bayan jawabi daga manyan shugabannin gidan Redio na Equity FM, KBTV, Sakataren din-din-dim na ma'aikatar wasanni da matasa, shugaban kungiyar yan Jarida na kasa reshen jihar Kebbi, sun ta'allaka bayanansu ne wajen godiya ga Gwamnatin jihar Kebbi kan amsa shirya wannan taron. Haka zalika sun fayyace dalla dalla yadda muhimmancin taron zai zama mai amfani ga yan Jarida da yan SMedia wajen gabatar da labarai.

Fitaccen masani kuma kwararre kan harkar ingizo da silasilar satan bayanan sirri na na'urorin zamani Muhammad Nasir, ya nuna yadda ake satar amshe ragamar na'urorin zamani kamar su wayar salula, Kwamputa da sauransu, wanda haka na faruwa ne sakamakon yadda maharan sukan shirya cutar na'ura watau VIRUS, kuma su aika ma wanda suke bukatar satar bayanansa ko amshe ragamar na'urarsa.

Muhammad ya nuna a zahiri yadda lamarin ke faruwa, da matakai dalla dalla yadda ake yi har hakan ta kasance.

A nashi gabatarwa, kwararre kuma shahararren dan Jarida  Abdallah Elkurabe, ya fahimtar da mahalarta taron kan yadda ya kamata a tafiyar da aikin jarida, tsare tsare, ka'idodi, da ababen da ya kamata a kaurace wa amfani da su a lokacin rubuta rahotu, musamman ga yan SMedia.

Hakazalika, Sakataren din-din-dim na ma'aikatan Sadarwa na jihar Kebbi Alhaji Hamisu Garba Zuru, ya fahimtar ne ta yin bita ga yadda ya kamata a rubuta rahotu, kan gabatar da labari, taken labari,ababen da ya kamata labari ya kunsa, tare da bayar da muhimmanci kan yadda mai rahotu zai kauce wa amfani da kalamai da za su iya tayar da zaune tsaye.

Za a ci gaba da wannan taron bita har zuwa ranar Juma'a 20 ga watan Disamba 2019.

Ku kasance tare da ISYAKU.COM domin kawo maku ingantaccen labari kan yadda taron ke kasancewa . 

Tuntube mu, rubuto ra'ayi ko ka aiko labari LATSA NAN

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN