Labari cikin hotuna: Duba abin da jama'a suka yi ma wani barawo a cikin kasuwa

Rana ta bace ma wani kusurgumin barawo bayan asirinsa ya tonu kuma jama'a suka yi masa dukan kawo wuka da ya kusan aika shi barzahu ranar Alhamis a cikin kasuwar Swali na jihar Bayelsa.

Wasu yan kasuwa sun yi yunkurin kona shi, amma sauran jama'a suka yi masa rana.

Ya zama wajibi matasa su rungumi sana'a kuma a daure a kaurace wa daukan dukiyar bayin Allah domin kauce wa irin wannan tozarta. Allah ya kiyaye mu da zuri'armu gaba daya.
  
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post