Labari cikin hotuna: An kashe jami'an tsaro 2 aka banka wa gawa da motarsu wuta

Ana zargin cewa an kashe wasu jami'an yansanda guda biyu a garin Oraifite a jihar Anambra lamari da ake kyautata zaton cewa yan kungiyar IPOB ne suka aikata.
Rahotanni sun ce ana zargin cewa jami'an tsaron sun harbi wasu yan kungiyar IPOB guda 4, lamari da ya sa suka mutu, sakamakon haka fusatattun yan kungiyar suka kai farmaki ga jami'an tsaron suka kashe biyu daga cikinsu kuma suka banka wa gawa tare da motarsu wuta.

Amma wani rahotun kuwa cewa ya yi, jami'an tsaron sun yi kokarin kama wasu mutane ne bayan wani mumunar fada da aka yi bayan wani jana'iza ranara Asabar, lamari da ya jawo kisan su jami'an tsaron.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post