Kasar Saudiya ta kayyade shekarun isa aure zuwa shekara 18 a fadin kasar

Kasar Saudiya ta yi sabuwar doka ta kayyade adadin shekarun aure zuwa shekara 18, dokar wacce ta fito ta hannun Ministan sharia na ksar ya ce auren yar kasa da shekara 18 ya haramta yanzu a Saudiya.

A wata takarda da ta fito daga ofishin Ministan shari'a wanda kuma shi ne shugaban majalisar koli kan harkar sharia Sheikh Dr. Walid Al-Samaani, ya umarci Kotunan kasar Saudiya su mika takardar neman aure na wadanda suka kasa shekara 18 zuwa Kotunan musamman, saboda a tabbatar cewa aure da za a yi ma yan kasa da shekara 18 ba zai cutar da su ba na miji ko mace.

Wannan sabuwar dokar tana daya daga cikin dokoki na musamman, wanda aka yi domin yin gyara ga fuskar dokokin kariya ga yara kanana a kasar Saudiya, bayan Majalisar Shoura ta zartar da dokar a watan Janairu 2019. An sami sauye sauye a dokokin Saudiya tun lokacin da Muhammad Bin Salman ya zama Yarima shekara biyu da suka gabata
 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN