Dasuki ya isa wajen iyalinsa bayan ya shaki iskan 'yanci | ISYAKU.COM

Tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro lokacin shugba Goodluck Jonthan watau Sambo Dasuki, ya hade da iyalinsa bayan shekara hudu yana tsare a hannun hukumar DSS.

Ranar 1 ga watan Disamba 2015 ne hukumar DSS ta kama Dasuki kuma ta tsare shi, daga bisani hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban Kotu bisa zargin tuhumarsa da hannu a badakalar sayen makamai na Dalan Amurka biliyan 2.1 karkashin mulkin Goodluck Jonathan.

Bayan ya cika ka'idodin belinsa da Kotu ta bayar ranar 29 ga watan Disamba 2015, DSS ta sake kama Dasuki.

Dasuki ya kasance a hannun hukumar DSS sai ranar 24 ga wataan Disamba 2019, bisa umarnin Atoni janar na Najeriya DSS ta saki Dasuki ranar Talata da dare. Daga bisani iyalan Dasuki sun tarabe shi a gidansa da ke Asokoro a babban birnin tarayya Abuja.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN