Yadda DSS ta saki Sowere daga karshe bayan kotu ta bayar da belinsa - Hotuna

Daga karshe, fadar gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sakin Omoyele Sowere bayan ya shafe watanni a hannun hukumar DSS. Tun farko Ministan sharia Abubakar Malami, ya fitar da sanarwar cewa fadar shugaban kasa ta bayar da umarnin sakin tsohon mai ba shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki, da Sowere.

Jaridar Legit Hausa, ta ruwaito cewa hukumar tsaro ta farar kaya DSS ta saki jagoran zanga-zangan juyin juya hali ta #RevolutionNow kuma ma wallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore.

A sakon da shafin Sahara Reporters na Twitter ya wallafa misalin karfe 6:12 na yammacin ranar Talata, 24 ga watan Disamba na nuna Sowore sanye da riga mai launin pink da wanda jeans mai launin bula tare da wani mutum sannan daga baya aka wallafa hotonsa a cikin mota.

Malami ya ce an saki Sowore ne sakamakon belin da wasu kotunna biyu suka ba su. Magoya bayan Sowore da wani lauya, Mista Abubakar Marshal da ke yi wa Mista Femi Falana aiki ne suka tarbi Sowore.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN