Inna lillahi: Wani lebura ya kashe uban gidansa a cikin gonarsa, karanta dalili | ISYAKU.COM

An yi ma wani tsohon ma'aikacin kampanin hakar man fetur na kasa NNPC Ibrahim Ajayi Allah, mai shekara 65 mumunan kisan gilla a cikin gonarsa a Oke-Oyi da ke karamar hukumar Illorin ta gabas a jihar Kwara.

Wani dan uwan mamacin Yakubu Abejide Allah ya tabbatar da kisan yayansa.

Sai dai wata majiya ta ce wani lebura da ke yi masa aiki a gonarsa ne ya sare shi da adda a wurare da dama, lamari da ya yi sanadin mutuwar sa.

Hakazalioka majiyar ta ce wanda ya yi kisan ya amsa laifin aikata kisan, ya ce shi bai san abin da ya faru ba har ya kashe uban gidan nashi. Ya kuma kara da cewa har uban gidan nashi ya yi alkawarin zai saye masa mota.

Tuni yansanda suka yi awon gaba da shi zuwa sashen ofishin CID na jihar Kwara, inda ake gudanar da bincike kan lamarin.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post