Yadda mumunan zargi ya sa matar aure ta yi zina da mai gadin gidansu | ISYAKU.COM

Wani lamari mai ban haushi ya faru da wata matar aure mai suna Zuwaira. Domin dai Zuwaira matar aure ce da ke tsananin zargin mijinta Alhaji Sani cewa yana lababawa cikin dare yana cin amanarta ta hanyar yin lalata da wata budurwa mai suna Fatima wacce ke yi masu aikin gida.

Wata rana, Zuwaira ta kasa hakuri, ta kasa natsuwa domin tunaninta a ko da yaushe sai kara cin gaba yake yi akan zargi da take yi wa mijinta na kasancewa fasiki.

Wata rana sai Fatima yar aikin gida ta yi tafiya ba tare da ta sami yin bankwana da mijin Zuwaira ba, domin tafiyar kwana daya ne kawai, kuma Alhaji Sani baya gida lokacin da za ta tafi.

Bayan karfe 11 na dare, sai Alhaji Sani ya shaida wa Zuwaira cewa zai tafi Palo ya kwanta, kamar yadda ya saba wani lokaci idan yana son ya kalli wani shirin talabijin ko labarai idan baya jin barci.

Bayan Alhaji Sani ya tafi Palo, sai matarsa Zuwaira ta sulale ta shige dakin Fatima yar aikin gida, sai ta kashe wutan fitilan kwai na dakin, kuma ta tube sumbur ta kwanta a kan gadon Fatima mai aikin gida.

Bayan dan wani lokaci, sai ta ji motsin wani ya lallabo cikin duhu ya zo kan gadon da take kwance kuma nan take ya fara jima'i da ita. Bayan ya yi inzali sau biyar, sai ya ce bari in dan huta sai in cike biyu ya zama bakwai da na saba yi.

Sai Zuwaira ta ce " Bayan ka yi sau biyar kuma kake neman ka kara guda biyu su zama bakwai? Allah ya tona asirinka yau, FASIKI, MUNAFUKI, MACIYI AMANA. Kana yi mini sau uku kullum amma kake yi wa Fatima sau bakwai. Yau asirinka ya tonu !!!".

Tap di jan, jin muryar Zuwaira , sai Musa mai gadi ya ce " Waiyo Allah, don Allah uwargida Zuwaira ki yi hakuri, nine Musa mai gadi! wallahi ban san ke ce ba domin na dauka Fatima ce mai aikin gida da muka saba fahimtar juna da ita".

DARASI

Mumunan zato na fasikanci tsakaninn ma'aurata yana daya daga cikin mumunan lamari da ke ruguza martabar rayuwar aure da ma'aurata wanda ke kai ga mumunan rabuwa wanda gyara ke wuya tsakanin uwa da uban yara ba tare da jama'a sun fahimci musabbabin da ya sa aka kasa fahimtar juna tsakanin miji da mata ba.

Tsananin zargi ya kai Zuwaira ga aikata zina tare da mai gadin gidansu, kuma ya more tsatsonta har abada, sakamakon haka martabar ta ya rushe a wajen shi, ga shi kuma ta aikata zina da take zargin mijinta yana aikatawa da yar aikin gidan alhalin ita ce yau aka yin zina da ita hakika.

Ya zama wajibi ma'aurata su kaurace wa zargin fasikanci ko wani abu makamancin haka a tsakaninsu. Matukar zargi ya shiga a zaman aure, idan ba a kai zukata nesa ba, har abada zaman aure ya lalace kenan, kuma gyaransa sai Allah.

Allah ya taimake mu ya sa mu gane kuma mu gyara. Allah ya kiyaye mu tare da zuri'ar mu gaba daya.

NB: Wannan labarin kage ne kawai, domin fadakarwa da ilmantarwa. Sunayen da muka yi amfani da su bamu nufin wani ko wata face domin nuni kawai da kyakkyawar manufa.

Isyaku Garba Zuru @isyakulabari

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post