Gwmanatin Buhari ta bankado farfesoshi guda 100 na bogi a jami’o’in Najeriya

Legit Hausa


Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta bankado wasu manyan malaman
jami'o'in Najeriya guda 100 masu darajar karatu ta Farfesa amma fa ta
bogi, kamar yadda shugaban hukumar kula da jami'o'in Najeriya, NUC, ya
bayyana.

Shugaban NUC, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya bayyana
hakane yayin wani taron shuwagabannin jami'o'in Najeriya daya gudana a
babban birnin tarayya Abuja, inda yace sun fallasa sunayen farfesoshin
a shafin yanar gizo na hukumar, haka zalika sun aika sunayensu ga
jami'o'in da suke koyarwa.

A yayin taron, Farfesa Rasheed ya bayyana
cewa hukumarsa ta wallafa ka'idojin da ake bukatar kowacce jami'a ta
cika kafin ta samu sahhalewar hukumar don gudanar da karatun digiri na
farko, digiri na biyu da sauran matakan karatu da ake yi a jami'o'i.

Haka zalika ya umarci shuwagabannin jami'o'in da su umarci duk wani
farfesa dake aiki a jami'arsu daya daura takardar shaidar karatunsa
gaba daya a shafin yanar gizon hukumar NUC, inda yace ta haka ne
hukumar zata kara yin tankade da rairaya don tantance sahihai daga
cikinsu da kuma na bogi.

Farfesan ya kara da yin kira ga shuwagabannin
jami'o'in dasu tabbata suna da cikakken alkalumman dalibansu da
malamansu, sa'annan su dinga yin takatsantsan wajen rattafa hannu kan
takardun shaidar kammala karatu da suke baiwa dalibai, inda yace
shugaban hukumar NYSC ya yi masa korafin yadda wasu dalibai na amfani
da takardun kammala karatu na bogi.

Bugu da kari ya ja kunnen shuwagabannin da su dakatar da al'adar nan da zaka ga malamin jami'a
yana koyarwa a jami'o'I barkatai, inda yace doka ta bashi daman
koyarwa a makarantu biyu ne kawai, haka zalika dole ne ba zai wuce
awanni 8 yana koyarwa a kowanne rana ba.

Daga karshe Farfesa Rasheed ya nemi shuwagabannin dasu bada gudunmuwa wajen ganin an kawar da cin hanci da rashawa daya dabaibaye bangaren karatu a matakin jami'a,
sa'annan ya basu kwarin gwiwar su kawo masa rahoton duk wani badakala
da suka ji.
Previous Post Next Post