• Labaran yau


  Shugaba Buhari ya bayar da umarnin a sake gaggauta daukan 'yan sanda 400,000

  Legit Hausa

  Ma'aikatar kula da harkokin da suka shafi rundunar 'yan sanda ta ce ta
  samu umarnin gagga wa daga fadar shugaban kasa a kan ta dauki sabbin
  'yan sanda 400,000 domin magance karancin da jami'an tsaro keda shi.

  Da yake sanar da hakan ranar Litinin, shugaban sashen hulda da jama'a
  na ma'aikatar, Odutayo Oluseyi, ya bayyana cewa tuni ministan
  ma'aikatar kula da harkokin 'yan sanda ya kafa kwamitin mutane 13
  domin fitar da tsarin yadda za a dauki karin sabbin jami'an.

  Umarnin fadar shugaban kasar ya kawo karshen tababar da ake yi a tsakanin
  hukumar kula da harkokin 'yan sanda (PSC) da kuma ofishin babban
  sifeton rundunar 'yan sanda (IGP) a kan waye yake da alhakin daukan
  sabbin jami'an 'yan sanda. Oluseye ya bayyana cewa kwamitin da
  ministan ya kafa ya kunshi mambobi daga PSC da kuma rundunar 'yan
  sanda.

  Ya kara da cewa aikin kwamitin shine fito da tsarin da za a yi
  amfani da shi wajen daukan sabbin jami'an bisa tsarin gwamnatin
  shugaba Buhari na bawa tsaro fifiko. A cewar Oluseye tuni minista
  Dingyadi ya rantsar da kwamitin tare da sanar da cewa daukan sabbin
  jami'an na daga cikin shawarwarin da kwamitin mataimakin shugaban
  kasa,

  Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayar a kan aiyukan da ya kamata
  gwamnati ta bawa fifiko domin cimma manufofinta kamar yadda ta dauki
  alkawari tun lokacin yakin neman zabe. Shugaba Buhari ne ya kafa
  kwamiti a karkashin Osinbajo domin duba nasarorin da gwamnatinsu ta
  samu da kuma haska mata bangarorin da ya kamata ta mayar da hankali a
  zangonta na karshe, daga 2019 zuwa 2023.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Shugaba Buhari ya bayar da umarnin a sake gaggauta daukan 'yan sanda 400,000 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama