Cika shekara 30 da auren Buhari da Aisha, tarihin 'ya'yan da Aisha ta haifa wa Buhari

Legit Hausa

A yau ne aka cika shekaru 30 da auren Hajiya Aisha Muhammadu Buhari da
kuma Sahibarsa, Aisha Buhari. Mun kawo maku jerin Iyalin da shugaban
kasar ya samu tare da Mai dakinsa.

1. Halima Buhari An haifi Halima-Sheriff ne a karshen shekarar 1990. Halima ta yi karatunta a
gida Kaduna da kasashen ketare inda ta je har Kwalejin Bellerby da
Jami'ar Leicester duk da ke Ingila. Halima ta zama Lauya a tsakiyar
shekarar 2016, kuma ta na auren Babagana Muhammad Sheriff tun 2012.

2.Yusuf Buhari Yusuf Buhari ne babban 'Da kuma Namijin da kurum Hajiya
Aisha Buhari ta haifa a Duniya. An haifi Yusuf ne shekaru 27 da su ka
wuce. Yusuf ya yi karatu jami'ar Surrey ta Ingila tare da 'Yanuwansa,
ya kuma yi bautar kasa a gida. Shi ne 'Da namijin da Buhari ya mallaka
a yanzu.

3. Zahra Buhari Zahra Buhari-Indimi ce wanda ta fi fice a
cikin 'Ya 'yan shugaban kasar. Jama'a sun fara sanin Zahra ne daf da
zaben 2015. Zahra ta yi karatu ne tare da 'Yanuwanta. An haifi Zahra
ne a Ranar 18 ga Disamban 1994. Ta auri Ahmed Muhammad Indimi ta na da
shekaru 22 a Duniya.

4. Aisha Buhari Aisha Buhari ce 'Diyar Uwargidar
Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta hudu. An fi kiran Aisha da Hanan domin
a sakaya sunan Mahafiyarta. An haifi Hannan ne a karshen Agustan 1998.
Wannan ya na nufin 'Yar karamar Aisha Buhari ta na da shekaru 21.
Hannan ta na sha'awar daukar hoto.

5. Amina Buhari Amina Buhari mai
shek aru 15 da haihuwa ce 'Yar autar shugaba Buhari da Mai dakinsa.
Kamar yadda Jaridar Premium Times ta taba kawo rahoto kwanaki, ana yi
wa 'Yar autar da Noor. Noor da 'Yaruwarta Hannan ba su yi aure ba
tukuna. A da can, su na karatunsu ne a Garin Kaduna.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN