Wani bawan Allah ya kwara wa matarsa tafasashshen ruwan zafi, karanta dalili | ISYAKU.COM

Wani mutum mai tsananin kishi ya raunata tsohuwar matarshi bayan ya watsa mata tafasashshen ruwan zafi hade da man girki. Rahotanni sun ce wannan dan talikin mai matsakaicin shekaru ya sami matarsa ne a wani waje a Kiembeni ya aikata wannan aiki.

Jaridai Legit Hausa, ta ruwaito cewa, wata mata mai shekaru 24 ta salube bayan da mijinta ya watsa mata tafasasshen ruwa hade da soyayyen man girki. Matar mai suna Winnie Wambua ta yi ikirarin cewa, tsohon mijin nata mai matsakaicin shekaru mai suna Henry Mugonda, sun rabu dashi ne fiye da shekara daya da ta shude.

Ya risketa ne a wajen gyaran jiki a Kiembeni, yankin Kisauni, kuma ya bukaci ta dawo su cigaba da zaman aurensu. A kalamanta, “A ranar 13 ga watan Disamba, ya zo wajen aikina kuma ya bukaceni da in koma aurenshi. Kamar dai yadda na saba, na ce mishi a’a.

Ai kuwa hakan ya harzuka shi kuma ya ce min sai ya tabbatar da na wahala kamar yadda yake jin radadin rasa ni a rayuwarshi. “Bayan kamar mintuna 30, ya koma wajen gyaran jikin dauke da babban kofi da ke kunshe da ruwan zafi da soyayyen man girki.

A nan take ya wankeni da wannan abun dake cikin kofin,” cewar Wambua. Ta kara da cewa, “kamar yadda ya bayyana a aikace, ya shirya hakan tuntuni.” Tuni dai aka cafke wanda ake zargin. 

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post