Fitacciyar Jaruman Finafinan Bollywood na kasar India Gita Siddharth Kak ta mutu ranar 14 ga watan Disamba a Mumbai. Jarumar ta fara fice ne a wani shahararren Fim na mai shirya finafinai M.S Sathyu a fim dinsa na 1973 watau "Garam Haya"
Ta kuma yi fice tare da samun kyauta da daukaka a gida India da kasashen Duniya, tare da samun lambobin girma da na yabo. Musamman a matsayin da ta fito Amina a fim din Gita a fim da Gulzar ya shirya a 1972 watau "Parichay" tare da Jarumai Jeetendra da Jaya Bhaduri.
Jarumar ta yi fice a finafinan shekarun 1970's da 1980's inda ta fito a finafinai kamar "Sholay", "Trishul", "Disco
Dancer", "Ram Teri Ganga Maili", "Nooriea, "Desh Premee", "Dance Dance",
"Kasam Paida Karne Wale Ki", "Shaukeen", "Arth", aceMandi", "Ek Chadar
Maili Si", "Gaman" da "Doosra Aadmi".
Gita ta auri mai gabatar da shirye shiryen Talabijin kuma mai shirya fina finai Siddharth Kak wanda aka fi sani a shirin Talabijin da Mujalla "Surubhi" wanda ake watsawa a Doordarshan daga 1990 zuwa 2001.
Ta mutu ta bar diya mai suna Antara wacce ke gabatar da shirye shiryen Talabijin.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari