Rikicin APC: Jerin sunayen gwamnoni 4 da suka yi yunkurin cire Oshiomhole | ISYAKU.COM

Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyar APC na kasa ya sha da kyar bayan wani yunkuri da wasu gwamnoni suka yi domin a tsige shi daga nukamin shugaban jam'iyar sakamakon wani tattaunawa da aka gudana\r tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da wasu Gwamnonin jam'iyar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wasu Gwamnoni sun yi kokarin tsige Oshiomhole, amma sai Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya ceto shi saboda ya dago shirin kuma ya bata shi.

Rahotun ya bayyana sunayen gwamnonin da suka kitsa cire Oshiomhole daga kujerarsa wadanda suka hada da:

1.Kayode Fayemi - Ekiti
2. Nasir El-Rufai - Kaduna
3. Abubakar Badaru - Jigawa
4. Atiku Bagudu - Kebbi

Rahoton har ila yau, ya kara da cewa, Gwamna Zulum ya shaida wa shugaba Buhari cewa, Gwamnonin sun shirya cire Oshiomhole ne domin su sa daya daga cikinsu a matsayin shugaban jam'iyar APC saboda daya daga cikinsu ya karbi shugabanci shugaban kasa a 2023.

Zulum ya gaya wa Buhari cewa " Zancen shugabaci ne 2023, suna bukatar wanda za su juya shi kamar yadda suka ga dama, shi ya sa suka bukatar Oshiomhole ya bar kujerar".

Hakazalika rahoton ya kara da cewa, Buhari na sane da shirin, kwana daya kafin a gudanar da taron, inda El-rufai ya gaya wa Buhari cewa suna son a cire Oshiomhole ne daga mukaminsa sakamakon gazawa wajen tafiyar da shugabancin jam'iyar.

Yayin da yake jawabi a wajen tattaunawar, Gwamna Zulum ya gaya wa Buhari cewa " Su waye Gwamnonin APC da ke tare da kai, kuma yaushe kuma a ina muka tattauna cewa shugaban jam'iya ya yi murabus?".

Rahotanni sun ce Zulum ya gaya wa shugaba Buhari cewa kada ya aminta da wadannan Gwamnonin guda hudu, ya kuma gaya wa Buhari cewa Gwamnan jihar Kebbi Bagudu, ya taba rokonsa cewa ya goyi bayan tsohon Gwamnan Zamfara Abdul-azeez Yari domin ya maye gurbin Oshiomhole.

Hakazalika rahotanni sun ce, Zulum ya kalubalanci Gwamna Bagudu na jihar Kebbi cewa ya karyata shi.

" Mai girma shugaban kasa duk abin da wadannan Gwamnoni da suke son a cire Oshiomhole suna yin haka ne domin suna da burin son su zama shugaban kasa a 2023". Daga bisani Buhari ya fice daga dakin tattaunawar, yayin da masu son a cire Oshiomhole suka ci gaba da neman jiga jigan APC 120 domin su mara masu baya. Masu goyon bayan Oshiomhole suka ci gaba da kare shi, sun hada da Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Dapo Abiodun (Ogun) da Gboyega Oyetola
(Osun).

Gwamnonin da ke son a cire Oshiomhole suna son a maye gurbinsa ne da tsohon Gwamnan jihar Zaamfara Abdul-azeez Yari.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN