DPO na yansanda da aka sace a wata jijhar Arewa ya kubuta

Yan bindiga sun saki Ahijo Muhammad wanda shi ne DPO na yansanda a garin Mubi. An sace Ahijo ne yan makonni da suka gabata yayin da yake kan hanyaarsa daga Yola zuwa Mubi a jihar Adamawa.
 
Rahotanni daga rundunar yansanda a Adamawa, sun ce jami'an yansanda sashen PuffAder da Operation Farauta ne suka jagoranci farutan wadanda suka sace DPO, sakamakon haka suka kubutar da shi a Mubi.

Maharan sun saki Ahijo ba tare da wani rauni ba, yayin da yansanda suka shiga bincike domin zakulo wadanda suka aikata aika aikan.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post