Rikicin jihar Zamfara: Gwamna Matawalle ya dauki babban mataki domin kawo karshen lamarin

Legit Hausa


Mun samu labari Mai girma Bello Matawalle ya sanar da matakin da
gwamnatinsa ta dauka na karbe duka filayen da aka raba domin kafa
wuraren kiwon dabbobi tun daga 1999 zuwa yanzu.

Darekta Janar na yada labarai na jihar Zamfara, Yusuf Idris, ya bada wannan sanarwa a Ranar
Asabar, 30 ga Watan Nuwamban 2019. Hakan na zuwa ne bayan wasu
sababbin kashe-kashe. Idan ba ku manta ba a cikin 'yan kwanakin nan,
aka kashe akalla mutum 14, haka zalika an jikkata wasu fiye da mutum
10. Wannan ta'adi ya auku ne a Garin karaye da ke Garin Gummi.

Wannan ne karon farko da 'yan ta'adda su ka sabawa yarjejeniyar sulhun da aka
yi da gwamnatin jihar. Wannan ya sa gwamnan Zamfara ya dauki matakin
janye filayen noma da ke cikin jihar. Kamar yadda jawabin da aka fitar
a karshen makon nan ya nuna, gwamnan ya ce wannan mataki ya zama dole
domin shawo karshen matsanancin rikicin da ake fama da shi a Zamfara.

Gwamnatin Mai girma Bello Matawalle ta nuna cewa kashe-kashen da ake
faman yi a jihar, bai rasa nasaba da filayen da aka ware domin kiwon
dabbobi da noma a jihar a lokutan baya. A jawabin da Idris ya fitar,
ya bayyana cewa za a sake rabo filayen kiwo a jihar nan ba da dadewa
ba.

An nada wani kwamiti na musamman da zai yi wannan aiki, ya mikawa
gwamnatin rahoto. "Karbe filayen gona da aka yi zai fara aiki ne ba
tare da wata-wata ba. Kuma ana kira ga duk wanda wannan ya shafa, su
yi biyayya ga umarnin gwamnati." Inji Mai girma Gwamnan jihar.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN