An kama yansanda 5 da suka yi harbi da ya kashe mutum a Lagos

Rundunar yansandan jihar Lagos ta kama wasu jami'an yansanda guda biyar da ake zargin sun kashe wani matashi mai suna Maliki Muhammed mai shekara 27 suka kuma jikata wasu mutum biyu a Oshodi.

Ana zargin cewa jami'an yansandan ne suka yi harbi a wani gidan rawa Crest Inn Club da dare, sakamakon haka Maliki ya rasa ransa. Jami'an yansandan sune  Inspector Orubu Olusola; Inspector Apalowo Ola; Inspector Kasai Sule; Sergeant Momoh Ogwuche da Sergeant Adoga Collins.

Kakakin hukumar yansandan jijhar Lagos DSP Bala Elkana ya tabbatar da kama jami'an yansandan wadanda ke aiki a sashen rundunar yansanda na Akinpume karkashin kulawar DSP Oloko Wale, DPO da ASP Adamu Babajo

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post