Cikin hotuna: Yadda aka kama yan fashi da suka shiga Bankin First Bank a Abuja

Hotunan yan fashi da suka je yin fashi da makami a Bankin First Bank da ke garin Mpape a babban birnin tarayya Abuja ranar Asabar 28 ga watan Disamba ya bayyana.

Rahotannin farko sun ce wasu yan fashi da makami sun shiga Bankin First Bank da ke Mpape, nan take aka sanar da jamai'an tsaro wanda ya hada da sojoji da yansanda kuma suka zagaye Bankin.

Hakazalika wata majiya ta ce yayin da daya daga cikin yan fashin ya yi kokarin fita daga Bankin sai jamai'an tsaro suka harbe shi kuma ya koma cikin Bankin jina jina kuma daga bisani ya mutu.

Daga karshe jami'an tsaron sun afka cikin Bankin kuma sun kama duk yan fashin su hudu har da wani ma'aikacin Bankin da yake ba yan fashin bayanan sirri, kamar yadda Kwamishinan yansandan FCT Bala Ciroma ya tabbatar.

Kalli hotuna a kasa: 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN