Allah wadai: Kanin uba ya kashe dansa saboda budurwa , karanta adalili

Rahotun Isyaku Garba Zuru 29-12-2019

Wani kanin uba wanda tsananin kishi ya rufe masa ido ya kashe dan shi saboda dan nashi ya sami wata yar hatsaniya da budurwar kanin uban a kauyen Abayi da ke karamar hukumar Osisioma a jihar Abia. Iyalin Eli da jama'ar kauyen sun wayi gari cikin bakin cikin ganin cewa Chimezie Eli dan shekara 45 wanda kanin uba ne ya kashe dansa Samuel Chimere Eli mai shekara 23.

Rahotanni sun ce Samuel wanda ke aji na karshe a Kwalejin ilimin kimiyya da fasaha ta jihar Abia (ASCETA) ya dawo gida daga  garin Umuahia domin ya yi bikin Kirsimeti a kauyensu ranar 24 ga watan Disamba. Amma cikin datre sai wata gardama ta tashi tsakaninsa da budurwar kanin ubansa.

Daga bisani an sasanta budurwar kanin ubansa da shi Samuel. Amma bayan kowa ya watse, sai Samuel ya shiga daki ya kwanta domin ya yi barci. Sai kanin uban ya shiga dakin ya caka ma dansa Samuel wuka a kirji, sakamakon haka jini ya dinga malala.

Mun samo cewa kanin uban ya fice daga dakin, amma Samuel ya yi kokari ya taimaki kansa duk da cewa jini yana ta bulbulowa daga kirjinsa. Da haka ya yi kokari ya isa wajen da zai sami mota, aamma kafin a isa Asibiti da shi ya riga ya mutu a kan hanya saboda jini ya kare a jikinsa.

Jaridar TheNation ta ruwaito cewa an kama kanin uban Samuel watau Chimezie, kuma yana ofishin CID inda yake amsa tambayoyi.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN