Gwanatin Jigawa ta tallafa wa mata 440 da bashin bunsuru da awaki

Gwamnatin jihar Jigawa ta tallafa wa mata 440 da bashin Awaki a karamar hukumar Birniwa karkashin shirin gwamnatin jihar da za ta taimaka wa mata da rance awaki 1,320.

NAN ta ruwaito cewa shugaban kwamitin rabon Awakin Ahmed Zubairu ya fadi haka a Birniwa ranar Juma'a bayan an kammala tantance rukunin farko na wadanda za su amfana da shirin.

Zubairu ya ce mata daga mazabu 11 za su amfana da wannan rance wanda za a biya a cikin wata 18.

Ya ce kowace mace za ta sami Bunsuru guda daya da Akuya biyu domin su yi kiwo.

Ya kuma ce sharuddan karbar bashin awakin ya hada da yarda da cewa za a biya bashin, nuna shaidan cewa mace yar asalin yankin ne, kuma cewa wannan ne karo na farko da matan za su amfana da shirin.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN