Rahotun TRT Hausa
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Sojojin China sun yi gwajin sabon makami mai linzami samfurin JL-3 mai karfin isa ko'ina cikin Amurka.
Kamfanin
dillancin labarai na Sputnik ya bayyana cewa Jaridar Washington
Times wacce ta ta rawaito wata majiyar Pentagon na cewa an gwada makamin
mai linzami ranar 22 ga watan Disamba a Bohai Bay dake arewa maso
yammacin tekun Bahar Maliya.
Labaran da aka fitar sun bayyana cewa an bi diddigin tauraron dan adam na Amurka.
Ba a bayar da karin bayani game da lamarin ba.
Kyaftin
din sojan Amurka da ya yi ritaya James Fanell ya ce wannan aikin yana
nuna cewa China na da niyyar ci gaba da sanya Amurka cikin barazanar
kera makaman nukiliya.
Labaran sun ce a cikin shekaru biyu da suka gabata an yi gwajin makami mai linzami samfurin JL-3 akalla sau 4.