Waiwaye: Sakon Kirsimeti da Sardauna ya aika wa Kiristocin arewa a 1959 | ISYAKU.COM

Rahotun Legit Hausa

A yayin da shugabanni da jagorori ke cigaba da aka sakon taya Kiristoci murnar zagayowar ranar bikin Kirsimeti na shekarar 2019, Legit.ng ta yi wawaye 'adon tafiya' domin kawo sakon taya murna da firaministan yankin arewa, marigayi Ahmadu Bello, ya aika wa Kiristocin arewa a shekarar 1959.

A rubutaccen sakon na Sardauna ya bayyana cewa, "mutane ne mu da muka fito daga kabilu, addinai da al'adu daban-daban, amma kuma zaman tare ya hada mu wuri guda domin zama a matsayin al'ummar kasa daya.

"Duk da muna da banbance a hanyoyi da dama, abubuwan da suka hada mu zama wuri guda sun fi wadanda suka banbanta mu. "

A duk lokaci irin wannan, na kan yiwa jama'a tuni a kan bukatar mu kasance masu hakuri da juna saboda banbancin addinin dake tsakaninmu.

"Bamu da wata manufa ta nuna fifiko ga wani addini fiye da wani, jama'a kan iya dogaro ga wannan tabbaci da na bayar. "Zamu kare mutuncin duk wani addini da mabiyansa matukar babu saba wa dokokin kundin tsarin mulki, a bisa dogaro da haka nake mika sakon taya murna, amadadina da na ministocina, ga mabiya addinin Kirista a wannan babbar rana.

"Lokaci ya yi da zamu jingine banbancinmu na addini a gefe domin mayar da hankali tare da hada kai wajen samun cigaban kasarmu."

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN