Rahotun TRT Hausa
Mutane 11 ne
sula rasa rayukansu sakamakon rikicin da aka yi tsakanin 'yan kasuwa da
wasu bata-gari a Banjui Babban Birnin Jamhuriyar Aflrka ta Tsakiya.
Labaran
da jaridun kasar suka fitar sun ce an samu rikici tskanon 'yan kasuwa
da 'yan tawaye kan biyan haraji a unguwar PK5 da mafiya mazaunanta
Musulmi ne.
Sakamakon rikicin an kashe mutane 11 tare da jikkata wasu ds dama inda aka kuma kona shaguna da wuraren sana'a.
Duk
da yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanya hannu a kai a kasar a 2012
amma har yanzu an kasa zama lafiya a Banjui da wasu yankunan kasar.
A
shekarar 2013 an gwabza rikici da ya koma yakin basasa tsakanin
Kiristocin Anti-Balaka da Musulmi mafiya rinjaye Seleka inda aka kashe
dubunnan mutane.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari