Yajin aikin NUEE: Birnin kebbi da kewaye na fuskantar rashin wutan lantarki

Da karfe 12 na safiyar Laraba, garin Birnin kebbi da kewaye ya fuskanci daukewar wutan lantarki sakamakon wani yajin aiki da kungiyar ma'aikatan wutan lantaki National Union of Elecricity Employees NUEE ta jagoranta.

Mujallar ISYAKU.COM ya gano cewa ofishin kampanin KEDCO na garin Gwadangaji, da na Unguwar Rafin Atiku duka a rufe suke. Haka zalika babban ofishin da ke GRA NEPA a unguwar Tudun wada Birnin kebbi shi ma a rufe face wasu manyan hafsoshin kampanin da wakilinmu ya gani suna kai kawo a cikin harabar kampanin.

Sai dai wata majiya mai karfi, ta shaida mana cewa, daya reshen kungiyoyin wutan lantarki Senior Staff Association of Electricity & Allied Companies SSAEC  bata shiga wannan yajin aiki ba.

Wakilin mu ya tattaro cewa wannan yana nufin sai idan uwar kungiyar ta kasa ta janye yajin aiki, idan ba haka ba, ba abin da ofishin su reshen jihar Kebbi zai iya yi kan lamarin kasancewa ofishin kamar kowane ofishin ma'aikatar yana biyayya ne ga uwar kungiya ta kasa.

Wannan ya zo ne a bazata ga wasu masu amfani da wutan lantarkin, bayan wasu jama'a sun yi korafin cewa KEDCO ya kamata ta bayar da sanarwa a kafofin watsa labarai cewa za a dauke wutan lantarki sakamakon yajin aikin uwar kungiyarsu ta kasa, domin jama'a su yi wadataccen tanadi domin fuskantar yanayi na rashin wutan.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post