An kori wani tsoho daga garinsu bayan ya yi wa diyarshi ciki ta haihu sau 2

Wata al'umman kasar Okofia, da ke Otolo Nnewi a cikin jihar Anambra a yammacin Najeriya, ta kori wani mutum mai fiye da shekara 60 a Duniya daga garin da kasarsu gaba daya bayan ya yi wa diyarshi ciki har ta haihu sau biyu.

Wannan tsoho dan asalin kasar Okijia ne da ke karamar hukumar Ihiala. Jama'a sun daura wa tsohon ganyen icen Kwakwa wanda ke nuna la'ana da tur da matsayinsa, kuma suka daure shi da igiya a wuya wanda ke nuna tozarci.

Hakazalika an daurawa diyar ganyen icen Kwakwa yayin da take rungume da jariri da ta haifa wa mahaifinta.

Daga bisani wasu matasa suka tasa keyarsu zuwa cikin wata motar bas wadda ke jira a kan titi, yayin da wasu matasa ke amfani da tsintsiyan Kwakwa suna shere tafin kafafun da tsohon da diyarshi suka taka yayin da suke barin garin zuwa cikin mota, bisa camfin cewa suna share mugun abin da tsohon da diyarshi suka aikata ne a garin.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post