Abubakar ABK ya ba da kyautar littafai mai taken "WHY ME" ga makarantun jihar Kebbi

Fitaccen Marubuci kuma dan Jarida, Komared (Comrade) Abubakar Muhammed ABK ya mika kofin littafai da ya wallafa mai suna "WHY ME" ga Ma'aikatan ilimi na jihar Kebbi.

Shugaban sashen harsuna na ma'aikatan ilimi na jihar Kebbi Adamu Gado Usman ya raba littafan ga daliban Makarantar Sakandare na Gwamnati da ke Basaura. Ya kuma yi maraba tare da jinjina wa Marubucin littafin bisa wannan aikin kirki da taimako da Abubakar ABK ya yi wa daliban jihar Kebbi.

Ya kuma kara da cewa littafin misali ne na nassarori, kalubale tare da manuniya ga mafita da zai ilmantar tare da fadakar da dalibai domin haka zai sa dalibai su zama masu zimma da amfani mai ma'ana a cikin al'umma.

An raba kofin littafan ga duk makarantun Sakandare na jihar Kebbi karkashin kulawan ma'aikatan ilimi na jihar Kebbi.

Abubakar Muhammed ABK, Mawallafin littafan harshen Turanci, dan Jarida ne kuma wani jigo a kungiyar Marubuta da mawallafa na jihar Kebbi, hakazalika, jigo ne a kungiyar Masu yin finafinai na Arewa reshen jihar Kebbi. Abubakar ABK ya sha wallafa littafai kuma ya raba su bisa jinkai don amfanin al'umma da ci gaban jihar Kebbi da kasar Arewacin Najeriya.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post