An gano cibiyar koyar da damfara "Yahoo Academy" an kama dalibai da malamai


Jami'an hukumar EFCC reshen Uyo tare da hadin guiwa da jami'an ta na Abuja sun kaddamar da wani samame a wata cibiya da ake kira cibiyar koyar da damfara na "YAHOO ACADEMY" a unguwar Essien  da ke kauyen Ikot a karamar hukumar Eket cikin jihar Akwa Ibom.

An kama dalibai 23 tare da malamansu. Dalibai da aka kama yan shekara 19 zuwa 35 ne. Kuma sun amsa laifinsu cewa suna koyon yadda ake damfara ne da ya jibanci satar bayanan sirri na harkar kudaden bayin Allah, soyayya domin damfara, da kuma damfara ta yanar gizo da sauransu.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post