• Labaran yau

  Melaye vs Adeyemi: APC ta yi wa PDP fintinkau a sakamakon kananan hukumomi 4 cikin 7

  Legit Hausa

  Smart Adeyemi, dan takarar jam'iyyar APC a zaben kujerar sanatar
  mazabar Kogi ta yamma yana gaba da Dino Melaye na jam'iyyar PDP a
  sakamakon kananan hukumomi hudu cikin bakwai da aka fitar kawo yanzu.
  Yayin da Adeyemi ya samu kuri'u 5,609 a kananan hukumomi hudun, Melaye
  ya na da kuri'u 1882 hakan na nuna akwai banbancin kuri'u 3,727
  tsakaninsu.

  A karamar hukumar Lokoja, Adeyemi ya samu kuri'u 4,659,
  Dino kuma ya samu 920. A Mopa Morou, dan takarar na jam'iyyar APC ya
  samu kuri'u 309 yayin da abokin karawarsa na PDP ya samu kuri'u tara
  tak.

  Duk da cewa Melaye ya samu rinjaye da kuri'u kalilan a Koton
  Karfe da Ijumu inda 'yan takarar biyu suka fito, kayen da ya sha a
  kananan hukumomi biyu sun yi masa illa a zaben. Melaye ya samu kuri'u
  376 a karamar hukumar Koton Kafe yayin da Adeyemi ya samu kuri'u 287.
  A Ijumu, dan takarar na PDP ya samu kuri'u 577 yayin da abokin
  karawarsa na APC ya samu kuri'u 364.

  A halin yanzu ana jiran sakamakon
  sauran kananan hukumomin a lokacin hada wannan rahoton. Hukumar zabe
  INEC ta bayyana zaben ranar 16 ga watan Nuwamba a matsayin wanda bai
  kammalu ba wato (inconclusive) kasancewar kuri'un da aka soke sunfi
  yawan wadanda wanda ke kan gaba ya bada tazara. Adeyemi ya samu jimla
  kuri'u 80,118 yayin da Melaye ya samu kuri'u 59,548. Hakan na nuna
  akwai tazarar 20,570 yayinda aka soke kuri'u 43,127.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Melaye vs Adeyemi: APC ta yi wa PDP fintinkau a sakamakon kananan hukumomi 4 cikin 7 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama