Abubuwa 5 da baka sani ba game da wanda ya maka Dino Melaye da kasa a zaben Kogi

Legit Hausa

1. Haihuwa

An haifi Smart Adeyami ne daf da Najeriya za ta samu
'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, a Ranar 18 ga Agustan 1960.
Wannan na nufin Sanatan ya na da shekaru 59 yanzu a Duniya.

2. Karatuda aiki

Smart Adeyami ya yi karatu a Garinsu har ya zarce ya zuwa
Makarantun gaba da Sakandare. Adeyami ya samu shaidar PGD a bangaren
hulda da jama'a. Sannan kuma ya na da Difloma a fannin shari'a da wata
babbar diflomar a sha'anin yada labarai wanda ya sa ya zama 'Dan
jarida. Shafinsa na Wikipedia ya nuna Adeyamu ya yi karatun Digirgir
watau Masters a bangaren hulda da jama'a da ya samu shaidar PGD. Ya yi
wannan karatu ne a jami'ar fasahar tarayya ta Owerri. A bangaren aiki,
Smart Adeyami 'dan jarida ne kuma har ya rike shugaban kungiyar nan ta
'yan jaridan Najeriya na kasa baki daya. Adeyami ya rike wannan mukami
tun daga 1999 hae 2006.

3. Siyasa 2007 Bayan sauka daga kujerar NUJ,

Adeyami ya nemi takarar Sanata a mazabarsa ta Yammacin Kogi. An yi
dace ya yi nasarar zama 'dan majalisar dattawa, ya gaji Jonathan Tunde
Ogbeha a 2007.

2011

A shekarar 2011, Adeyami ya sake takarar 'Dan
majalisa a jam'iyyarsa ta PDP, ya kuma lashe zabe. Sai dai daga baya
kotu ta rusa zaben fitar da gwanin da jam'iyyar PDP ta shirya a
lokacin. Sanata Adeyami ya sake samun kyakkyawar galaba a kan babban
abokin hamayyarsa Abiye Abinso. Wannan ya sa koma kujerarsa. Ya kuma
rike mukamai a kwamitoci da dama a majalisar.

2015

Smart Adeyami bai samu sa'ar komawa majalisa a zaben 2015 ba, ya sha kashi ne a hannun
Dino Melaye na jam'iyyar APC. Daga baya kuma 'yan siyasan su ka yi
hannun riga da jam'iyyunsu.

2019

Bayan komawar Dino Melaye PDP, sai Smart Adeyami ya sheka APC. Dino ya sake lashe zaben 2019. Jim kadan
kotu su ka rusa wannan zabe na farkon 2019, su ka umarci a sake sabon
zabe. Smart Adeyemi ne ya lashe zaben da aka sake yi a Nuwamban 2019,
daga farko an gaza kammala zaben, amma a karshe INEC ta tabbatar
jam'iyyar APC ta yi nasara da ratar kuri'a fiye da 26, 200. Wannan na
nufin Sanatan da ya saba mikewa a zaure zai koma majalisar tarayya a
karo na uku.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN