Amana ta kama shi: Barawo ya kwace jakar wata budurwa garin gudu babur ya buge shi

Mun sami rahotun cewa babur ya buge wani matashi bayan ya sace jakar wata budurwa ya ruga da gudu, amma sai amana ta kama shi, domin dai babur ne ya buge shi kuma ya suma, cikin sauki mai jaka ta zo ta dauki jakarta.
Wannan lamari ya faru ne a kauyen Ajimele da ke jihar Delta. Bayanai sun ce ainihin barayin su biyu ne, amma ganin cewa babur ya buge abokin satarsa, daya daga cikin barayin sai ya kara gaba a guje ya bar abokinsa har jama'a suka rutsa da shi.

Bayan an yayyafa masa ruwa, barawon ya farfado, jama'a suka lafta masa na jaki har ya yi laushi, daga bisani suka mika shi ga yansanda.
 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post